@transcript ga ayyukan fassara da rubutun software a harshen wurin

Sama da shekaru goma, mu gwanaye ne a keɓaɓɓiyar fassara da sarrafawar ayyuka kan harsuna da rubutun software a harshen wurin.

Mu ƙware a kan rubutu a harshen wurin – wannan yana nuna daidaitawar software da rubuce-rubuce zuwa ƙa’idodin al’adun, harshen da fasahar kasuwa da aka yi niyya. Kuma mun yi ayyuka da suka shafi hanyar fassara, kamar su sarrafawar abin ciki, gwadawa ta yin amfani da aikace-aikace da aka yi fassara, ƙirar da sarrafawar wurin ajiyar kalmomi, da aikin DTP da zane-zane.

Kuma, za a iya daidaita ayyukanmu zuwa bukatun abokan cinikinmu. Suna ƙunshe da abubuwa da matuƙar inganci – da za a iya ƙara a cikin sarrafawar ayyukan gwani idan an bukata.

Muna zuba idon ayyukanku!